Follow Who Knows Road. Jiya a tattauna da akayi da Professor Isa Ali Pantami wanda Forum na AREWA YOUTH MENTORSHIP PROGRAM suka shirya kuma suka gabatar. Prof. Yayi ta nanata kallamar MENTORSHIP wanda a takardar shi me suna SKILLS IS RATHER THAN JUST DEGREE akwai shafi guda wanda prof. Yayi bayani sosai akan Mentorship, sannan ya jera duk wasu shahararrun masu kuɗi a duniyar mu na yau da mentors nasu. Sannan ya da misalai daban-daban aka irin gudunmawar da mentorship yake bayarwa. Maganar gaskiya bara kaje ko ina ba matukar baka da d mentor. Duk inda kake son zuwa wallahi wani ya rigaka zuwa, wani kamma yaje, ya dawo yasake komawa ya dawo, duk wani logic and obstacle na tafiyar ya sani. Don haka ka nime shi domin ya haka maka sai kama kaje. Shi Mentor mutun ne da zai baka wuyan shi, ka hau, domin ka kalla duk ina kake son gani. Bere gaji ba, sanna bere hanaka hawa ba. Rashin haka kuma zai samu hasarar lokacin mu da dukiyar mu. Don haka definitely follow who knows road at any condition. Allah yayi mana jagora Sanusi Abdulmanaf 6/9/23