@nearhausa.near na fadakar da illahirin masu amfani da wallet wallet da ake amfani da link wajen shigar su kamar my near wallet da meteor wallet da du dinga kula da ainihin url address din in sunzo shiga Google saboda yanzu ansamu wasu maha'inta masu cutar da al'umma suna satar irin url din wajen damfarar mutane wadanda basa kulawa wajen tantance ingancinsa da sahihancin url din near wallet ko meteor wallet din Saboda haka jama'a ayi a hankali a dinga ankarewa a yayin amfani da wadannan wallet don gudun fadawa hannu bata gari masu zambatar mutane yau da kullum kafin ayi wata mu'amala da wallet a tabbatar anduba URLs don a tabbatar da sahihancin url din in da akwai wani abu wanda mutum yaga bai gane ba to kada yayi kasa a gwiwa yaje shafin @nearhausa.near community da ke kan telegram yayin tambaya da wuri tun kafin yasa seed phrase din sa a wadannan sites din don tabbatar da sahihancin su ta hakane kawai mutum zai kiyaye kansa daga dana sani,