Alhamdulillah!❤️💜❤️ Assalamu Alaikum, Barkanmu da asuba. To Jama'armu yan Fafutuka/Gwagwarmaya ga wani abun alheri ya samu wanda naga bai dace ace banyi muku bayani ba! Sannan nasan indai kai dan "Crypto" ne kasan "Near Protocol Ecosystem" ko kuma nace "Near Protocol Project". To kamar yadda kuka sani a kwanakin baya nayi rubutu a lokacin da su malam Abdul-Hadee Isah Ibraheem suka samu aiki da "Near Protocol" wanda harma na danyi wasu bayanai dai akai. So, cikin yarda Ubangiji yanzu kuma "Near Protocol" zasu sake diban mutane wanda zasu jagorancesu a "Africa 🌍" baki daya bawai ma iya "Nigeria or Arewa" ba. Wani tsari sukai da ake kiransa da "NDC" yanzu, wanda sunyi hakanne domin magance wasu matsololi da suke fuskanta kamar a bangaren ", Community Treasury" nasu! In Shaa Allah zanyi muku bayani akan menene "Community Treasury" a nan gaba cikin wannan rubutun. So, yanzu zasu debi mutanan da zasuma leadership ne akan wannan sabon tsarin nasu na "NDC" da sukai. Amma kafin hakan shine suka fito da tsarin yin "Elections" wato za'ayi voting kafin su dauki mutum. Sannan kuma dole sai kana da account akan "Near Protocol Ecosystem" din nasu sannan zaka samu damar yin voting din. Bayan kabude account din kuma dole sai kayi wani "I'm human verification" wanda shine yake tabbatarwa da cewa kai mutum ne ba "Robot 🤖 ba". Domin idan basuyi hakan ba, to zai zamto ba'ai abunda ya kamaka ba. Sannan kuma wasu wasu iya amfani da "Bot" gurin jefa kuri'ar. Sannan kuma yau zasu dakatar da bayar da damar bude "Voting Account" da kuma "I'm human verification". Dan haka yanzu kafin rubutun yayi yawa bari na ajjiye muku links din da zaku shiga ku bude account din da kuma wanda zaku shiga shima bayan kunyi creating din "Near Protocol Wallet" din sai kayi "I'm human verification". 1] Create your"Near Protocol Wallet" here: https://app.mynearwallet.com/ 2] Do your "I'm human verification" here: https://i-am-human.app/?community=nearhausa&vertical=regionalcommunities Sannan kuma ga telegram group nan, wanda bayan ka bude "Near Protocol Wallet" din zakaje ka ajjiye "Account ID" dinka domin a turoma da "Gas Fee" wanda zakai amfani dashi gurin yin verification na "I'm Human Verification". 3] Telegram Group: https://t.me/NearHausa Shi "Account Id" din misali idan kazo gurin da zaka saka, sai ka saka sunanka misali; garbabala. To sai kawai kaje cikin wacen telegram group din kawai ka tura, "garbabala.near" shikenan zasu gani instantly sai su turoma da "Near Gas Fee" din. Duk wa yannan abubuwan instantly zaka yisu. Babu wahala ko kadan aciki. Sannan karubuta "Near Wallet Recovery Phrases" din da zasu baka idan kazo gurin "Create New Wallet". Sannan kuma "Account ID" dinnan da ka saka na sunanka shine kamar "Wallet Address" dinka. Sannan kuma in Shaa Allah zanyi video akai zuwa anjima idan akwai wanda naga basu gane yadda zasuyi creating account and do I'm human verification din. Amma yanzu kuyi shap-shap please kowa ya mallaki account dinsa domin yin voting din. A cikin wannan watan za'ai na "September" za'ai elections din. Gurbin mutanan da za'a diba sune kamar haka: 1] House Of Merit (15 seats) 2] Council Of Advisors (7 Seats) 3] Transparency Commission (7 Seats). Nasan wasu zasuce menene to wannan "House Of Merit, Council Of Advisors and Transparency Commission" dinnan, to nari kuji roles dinsu. 1] House Of Merit: Sune mutanan da zasu dinga planning na duk wani budget da "Near Protocol" zasuyi a Africa 🌍. Wato duk wani kudi da za'a fitar domin yin wani abu domin bunkasa "Ecosystem" din near protocol a Africa sai sun yarda kudin zai fita. Sannan sune suke da alhakin kashe koma nawane domin cigaban near protocol din. 2] Council Of Advisors: Su kuma sune masu bayar da shawarori akan yadda yakamata ayi da budget din idan "House Of Merit" sun fitar da kudi domin yin wani abu dan cigaban Near Protocol Ecosystem din. Da kuma tsare-tsare na wasu ka'idoji. 3] Transparency Commission: Su kuma sune mutanan da zasu dinga kula da roles din duk wani ma'ai kaci a nan "Africa" ta bangaren gurbinsa akan cewa shinkon yanayin abunda ya kama ko kuma bai cancanci da gurbin da aka bashiba. Da kuma bawa "Ecosystem" din da near protocol daga duk kanin wasu illoli na cutarwa ga near protocol din. Sannan "Transparency Commission" suna da bawar da zasu iya cire kowa wanne ma'ai kaci da aka samu da wani "Ha'inci" ko kuma cin amana a role dinsa, wato gurbin sa. Now in a very simple terms shine: House of Merit — budget planning. Council of Advisors — HoM budget advice and VETO law. Transparency Commission — protects the ecosystem from harmful actors. So gaskiya wannan na karamin matsayi bane wanda in Shaa Allah idan mutananmu sukai dace aka daukesu zasu amfanar da al'umma akai sosai, tunda duk abunda sukeso na cigaba kawai kaddamarwa zasuyi. Dan haka dan ALLAH jama'ah kuyi kokari ku tsabi muta nanmu yan Arewa a wannan tafiyar. Sannan nima megidanane Engr Musa Adam yake sanar dani cewa yakamata muyi kokari ace mutananmu ne akan ya yannan roles din, domin ba karamin cigaban mu bane. Sannan shi daman already yanzu yana aiki da "Near Protocol" din. Duk wani abu dan gane da "Near Protocol Ecosystem" yasan dashi. Sai kuma magana da nayi akan "Community Treasury" nace zanyi bayani a wannan rubutun nawa. To bari shima na danyi bayani akai in briefly. Community Treasury: Community Treasury wani tsarine da duk wani Crypto Project yake dashi a lokacin da za'a kaddamar da "Tekonomics". Ma'ana kamar tsara adadin tokens din da yakamata a siyar a "Public Sale" da kuma adadin wanne tokens ne yakamata su "Team" din su rike, and how many for private rounds and so on. To su near protocol a Tekonomics dinsu 17.5% of the initial tokens is allocated to the "Development Of The Community And The Ecosystem Around The Near Protocol". Wannan shine takai taccen bayani akan "Community Treasury". Sannan kuma gurbin mutanan dana lissafa sune zasu jagoranci duk wa yannan abubuwan dana lissafa na bangaren fitar da kudi. Dan haka gaskiya kar muyi wasa da wannan damar. In Shaa Allah indai yazamto mutananmu ne yan arewa akai, to in Shaa Allah bawai iya suba, kowama zai amfana da hakan. Dan haka in Shaa Allah akwai mutananmu da zasu tsaya takarar, dan ALLAH muyi kokari mu tsabesu. Sannan kamar yadda nafada muku dole sai mutum yanada "Verified Account" sannan zasu bashi damar yin voting din. Dan haka kowa yayi kokari ya mallaki account din sannan kuma yayi "I'm Human Verification" din. Ga kuma telegram group nan da mutum zai tura Account ID dinsa nan domin a turomai da Gas Fee din da zaiyi minting nan gurin yin "I'm Human Verification" din. Wanna shine bayanin kawai. Sannan idan baka fashimci wani abuba to kawai kashiga cikin telegram group din kayi tambaya zaka samu answer dinka cikin sauri in Shaa Allah. Allah Ubangiji Yasa Mudace. #AminuDayyibZakariyya @nearhausa.near