Ina so in kara jan hankali mutane, Chain Signature ba karamin taimakawa web3 zai yi ba wajen maida amfani da manhajojin web3 cikin sauki. Wannan ci gaban ya shafi masu amfani da manhajoji (users) da kuma masu kirkirar wadannan manhajojin (developers) inda hakan zai bude sabuwar hanyar amfani, yin transactions da kuma kirkire-kirkire a kan open web. A taron da akayi BUIDL Asia a Seoul, Korea, Near Co-Founder da Near Foundation CEO illian Polosukhin ya sanar da kaddamar da lunching na Chain Signatures a Near ecosystems. @NearHausa