AI ko (Artificial Intelligence) yana nufin fasahar dan adam. Wato abinda dan adam ya halitta ko kirkira domin rage masa ayyuka ko saukakawa cikin sauri da kuma gaba-gadi(automatic) a cikin na'ura da kuma zahiri kamar robot. Kamar yadda dan adam ke da hange da hasashe haka Shima AI yake da nasa da hangen da hasashe.Fasahar AI suna amfani da Algorithm da kuma da kuma (sub discipline) na AI wato Machine Learning. Wanene Ilya Polosukhin: kwararren software engineer ne kuma shine mallakin Babban Project dinnan mai saukin alamari wato NearProtocol. Ilya Polosukhin: Yana daya daga cikin wayanda suka taimaka wajen kirkiro " Machine Learning and Natural Language Processing (NLP) and Artificial Intelligence " cikin shahararriyar dakardar nan "Attention Is All You Need" karkashin kamfanin Google shekarar 2017 wannan takarda (paper) ta yi bayani ne (Introducing) akan "Transformer Model dasauransu. Bayan barin sa kamfanin Google ya kirki Babban Ecosystem din nan wato NearProtocol kamar yadda na fada a sama, Ya kirkiro NearProtocol ne domin magance wasu matsaloli da AI ke fuskanta. Near Ecosystem sunyi amfani ne da Blockchain Operating System (BOS). Sunyi aiki da BOS ne domin samar da yanci a kafar Intenet wato Decentralized Application (Dapp)da samar features kamar smart contract execution, decentralized storage, Identity Management Dasauransu. Near Protocol yanzu a duniya itace a gaba wajen hada ko samar da AI da Blockchain a dunqule domin warware wasu masaloli na AI da Blockchain baki daya. Wannan hadin AI da Blockchain zata kawo wa duniyar AI da Blockchain Technology babban sauyi. @nearhausa.near