Zanyi magana akan abunda ya banbanta Near protocol da sauran networks din wato sharding strategy,nodes a kowani Blockchain nada aiki uku ne,nafarko processing na transaction,na biw kuma communicating na ingantaccen transaction,sannan na karshen shine karasa shi transaction da kuma aje history nashi transaction din.Amma dazaran shi network din yana kara girma, transaction yana zuwa yayi yawa wanda yana kawo congestion a network din,amma shi sharding strategy yazo da wani hanya wanda dazaran network na kara girma,nodes ma kara girma sukeyi,rarraba nodes din yakeyi ,wanda kowani node yana daukan transaction nasa daban inda yake rage congestion a maimakon node daya na daukan kowani transaction dazai shigo cikin network din.