A taron BUIDL Asia A birnin Seoul na Kasar Korea, Co-founder na NEAR Foundation kuma CEO Illia Polosukhin ya bayyana wani sabon tsari wanda zai taimaka wajen tabbatar da chain abstraction wato chain signatures. Wannan tsari abu ne mai ban sha’awa saboda yana bawa NEAR accounts, da smart contract damar yin transactions a kan ko wane irin blockchain. Wannan yana faruwa ne da taimakon wani network wai shi MPC wato ‘Multi Party Computation’. Hakan yana nufin NEAR accounts zasu iya yin transactions a kan wasu blockchains din kamar Bitcoin da Ethereum. Ga takaitaccen bayani a kan yadda yake aiki NEAR account, wanda zai iya zama smart contract zai nemi izini a wajen validators ko MPC nodes domin yin transactions a kan wasu blockchains din. Hakan yana yiwuwa ne ba tare da mutum ya sauka zuwa wancan blockchain din ba, kuma ba sai yana da account a wancan blockchain din ba. Da account daya, mutum zai yi hulda da blockchain kala kala.