NEAR ya sauwaka user experience inda a maimakon wallet address wanda yake kan tsarin alphanumeric wanda sauran blockchains suke amfani dashi kamar 0x9A466804Fd8A2d811cFE9866a3AD62a9740dD804, NEAR suna amfani da named account kamar abdoullfurya.near wanda yafi saukin ganewa da kuma saurin haddacewa. Bude account a NEAR bashi da wahala sam sam inda kai tsaye zaka iya bude shi kai tsaye ta hanyar amfani da email, ko Telegram sannan kuma yana da saurin wajen kammala transactions (kusan sakan 1.3) sannan bashi da tsada wajen transactions (kasa da cent 1) . Bai tsaya a nan ba, ta hanyar account abstraction, NEAR sun janye wa masu amfani dashi matsalolin da suke fuskanta a wasu blockchains din wajen siyan cryptocurrencies, wanda hakan ya kara usability da kuma tsaro ta hanyar Access key system. Bugu da kari, NEAR yana bada damar sarrafa accounts din da suke kan wasu blockchains din ta hanyar Chain signature @nearhausa