A yayin taron da a ka yi a ETHDenver a satin da ya gabata, an nuna cewa hadin gwiwa shine zai kawo ci gaba a duniya cryptocurrency. Banda crypto, NEAR ta zo da gaba daya ecosystem dinta zuwa wannan taro. Ga Takaitaccen bayani a kan abin da ya faru:-- Altan Tutar na NEAR FOUNDATION shine ya bude taron da bayanin sa mai taken “future of DeFi: NEAR protocols role and potential”. Altan yayi bayani a kan shirin NEAR a kan DeFi wanda yake bada muhimmanci a kan fragmentation da modularity. Near tana da niyyar zama platform me hada mutane da manhajojin DeFi a kan blockchain kala kala. Illia Polosukhin, CEO kuma Co-founder na NEAR Protocol, ya kara fashin baki a panel din da aka yi na Decentralized AGI summit inda yayi bayani a kan canjin da yake faruwa a AGI. Bai tsaya nan ba, yayi bayani a kan kirkirar AGI mai zaman kan sa da kuma abubuwan da hakan zai kawo a duniyar decentralization. Illia ya kara da bayani a kan kara habbaka fasahohin AI domin jin dadin community.