Smart Contracts on NEAR Protocol NEAR Protocol suna bayar da framework mai karfi inda developers zasu kirkiri decentralized applications dApps masu amfani da smart contracts kuma masu aiki a wajaje da yawa. Ga misalin manyan abubuwan da Smart Contracts a NEAR suke badawa ∆. Scalability: Sharding architecture na NEAR Protocol yana bawa smart contracts damar faruwa a tare, cikin hanzari kuma da tabbatar da cewa mutane da yawa zasu iya yin hada hada da yawa a lokaci a cikin sakan daya. Wannan damar, ta tabbatar da cewa manhajoji a kan NEAR zasu yi amfani komin yawan mutanen da suke kan su. ∆∆. Rashin Tsada: Tsarin tattalin arzikin NEAR yana tabbatar da cewa za’a iya yin duk hada hadar da za’a yi cikin kwanciyar hankali ba tare da ana tunanin tsada ba. Developers zasu iya rubuta smart contracts dinsu sannan suyi amfani da blockchain din ba tare da sunyi tunanin tsadar gas fee ba. Hakan ya kawo sauki gare su da kuma sauran mutane masu amfani da manhajojin. ∆∆∆. Tsaro: NEAR Protocol sun bada muhimmanci sosai ga tsaro, inda suka tabbatar da wani mechanism mai karfi domin bawa smart contracts tsaro da kuma magance matsalolin da zasu zo a gaba. Ta hanyar verification, auditing da kuma best practices na smart contract development, NEAR suna da niyyar kawo fage mai tsaro domin wallafa manhajoji masu yin aikin da aka kirkire su domin shi. da Sauransu @nearhausa