Qoqarin Near na Tabbatar da Chain Abstraction!!! Adaidai lokacinda Duniyar Crypto ke fama da halin ni 'yasu dan tabbatar dauwamemmen cigaba, a lokacin NEAR ke zuwa da gaggarumin fasaha dake daukan hankali da wasa kwakqalwa wajen magance matsalar. A lokacinda ake ganin akalar Duniya ya maida hankali kan hadin gwiwa dan kawo cigaba a Duniyar Crypto a taron da akayi a ETH-Denver a wasu kwanuka dasuka gabata, a daidai lokacin NEAR ta zo da gaba daya ecosystem dinta zuwa wannan taro dan kyakkyawar baje haja ta musamman, inda megirma Altan Tutar na NEAR FOUNDATION ya bude taron da bayanin sa mai taken “future of DeFi: NEAR protocols role and potential”. Altan yayi bayani a kan shirin NEAR a kan DeFi wanda yake bada muhimmanci a kan fragmentation da modularity. Near tana da niyyar zama platform me hada mutane da manhajojin DeFi a kan blockchain kala kala. Gudumawar NEAR bai takaita anan ba, inda shima makerin nan Illia Polosukhin, CEO kuma Co-founder na NEAR Protocol, ya kara fashin baki a panel din da aka yi na Decentralized AGI summit, inda yayi bayani a kan canjin da yake faruwa a AGI. Bai tsaya nan ba, yayi bayani a kan kirkirar AGI mai zaman kan sa da kuma abubuwan da hakan zai kawo a duniyar decentralization. Illia ya kara da bayani a kan kara habbaka fasahohin AI domin jin dadin community. Hakazalika yayin cigaba da jawabinsa, Illia ya kara da yin hira da Erik Voorhees a kan decentralization na AI. Sannan ya kara da bayani a kan digital self-sovereignty a zamanin AI kafin mai takarar shugaban kasar Amurka wato Robert F. Kennedy Jr ya hau kan mimbari domin kulle session din da jawabin sa. A yayin neman maslaha da samun mafita, an rufe qofar karshe ne da, COO na NEAR Foundation wato Chris Donovan, yayinda yayi jawabi mai ingani, inda ya nuna cewa Chain Abstraction shine abinda zai karya barrier wanda yake hana mutane shiga web3 sosai. Ya kara da cewa rabe-raben blockchains shine yake kara tokare sabbin shiga wajen amsar wannan fasahar ta web3. Idan a ka saukaka wa mutane hanyar shiga da kuma bawa developers saukin kirkire-kirkiren su a industry din gaba daya, toh karbuwar web3 zai karu sosai. Kuma hakan zai yiwu ne ta hanyar Chain Abstraction. #ChainAbstraction #ChainAbstraction Wannan fasaha Lalle zaitaka rawan gani wajen karkatar da aqalar Web2 dan kutsawa Web3 ganin yadda Maqera keda dama, hakama gamagarin mutane kan biya buqatunsu cikin sauqi da nishadi. Da samun cikakkakun bayanai, agarzayo shafukanmu na @NearHausa a kafafenmu sada zumunta. Semun jiku.