Kwatankwacin Near da sauran Manhajoji A daidai lokacin da Duniyar #BlockChain ke daukan hankali da chanja akalar Duniya daga Central authorities zuwa Pear to Pear Ko P2P ta hanyar decentralisation, manhajoji da dama sun dauki lokaci suna tsare-tsare dan inganta tsarin manhajarsu, baiwa users daman aiyukansu da hada-hadan su, da kuma Sauqaqawa mutane harqallarsu. Daga baya, Mr. Illia Polosukhin da Abokin aikinsa Alex Skidanov suka zo da Near inda ta samar da tsaruka na musamman ga Maqera da masu hada hadan yau da kullum akan Blockchain. Alaqanta Near da sauran Manhajoji, Near an ginashi ne akan tsarin da bashi da iyaka Ko adadin yawan da zai dauka na masu anfani dashi, face sauqaqa buqatu masu anfani dashi. Wannan na tabbatar da cewa babu tsammani kan cewa Manhajar Blockchain din na NEAR zai cika, kuma sauqin harajin anfani dashi zai cigaba da karyewa zuwa mafi qarancin qasa, sabanin sauran manhajoji da suke daukaka haraji, da qara mai kaimi da tsada wajen mu'amala da wannan manhajan. Sake tabbatar da wannan sauqin farashin harajin, ba dare ba rana Near na qara sauqaqa farashin Haraji da harkoki yau da kullum ga masu ta'amuli dashi, inda a matakin farko ya sauqaqa farashin sa kwatankwacin na Ethereum 0.001% Ko kusa da haka. Bai tsaya wajen sauqaqa hada - hada kawai ba, Near yazo da tsare-tsare da dama Kamar: - Inganta tsaro(Security) - Qirqire-qirqire(Development/Building) - Wassanni(Gaming) - Sauri(Scalability) da makamantansu. Haka nan anata tsare-tsare wajen inganta Manhajar Near yadda dokacin Jama'a zasucigaba da anfani dashi cikin sauki. Don samun cikakkakun bayanai akan abubuwanda suke tafiya a wannan manhaja, Kuyi maza maza ku qaraso @NearHausa batare da gajiyawa ba.