Near Digital Collective (N.D.C) Rungumar Ci gaba da kuma hadin gwiwa don cimma manufa A duniyar mu ta yanzu, alaka da hada hada tana komawa digital. Hadin gwiwa wajen yin wani project ya tashi daga haduwar mutane a fili, ya koma vrtual wato haduwa a yanar gizo. Near Digital Collective wata idea ce wadda take nuni ga yadda aka samu canji wajen hadin gwiwa a wannan karni na 21. Near digital collective na nufin wasu mutane, ko kungiyoyi wadanda suke aiki tare yawanci daga nesa wato ta yanar gizo(remotely). Wadannan mutane suna amfani da fasahohi kala kala wadanda suke basu ikon haduwa ta virtual domin cima burinsu. Koma bayan haduwa physically ita NDC tana rayuwa ne a duniyar yanar gizo . Daya daga cikin ayyanannun fasali na NDC shine sassauci wajen haduwa. Mambobin kungiyoyi suna iya kasancewa daga ko ina a fadin duniya, hakan yana bada ikon tara mutane masu baiwa kala kala domin cima wata mafita. Kimiyya da fasaha tana taka muhimmiyar rawa wajen bawa NDC fage domin aiki ba tare da matsala ba a bangarori kamar fasahohin sadarwa na video conference, tura sako da kuma fasahohi na hadin gwiwa. Wadannan abubuwa sune kashin bayan wadannan kungiyoyi saboda sun bada dama ga mambobi wajen yin aiki da kuma tura sako ba tare da bata lokaci ba a duk inda suke a fadin duniya. Bangarorin da NDC take taka muhimmiyar rawa Open-Source Software Development: Daya daga cikin misalai masu amfani daga NDC shine open source software community. Sun hada da developers daga duk fadin duniya wadanda suke aiki tare akan projects kala kala kamar Linux Operating system da kuma Firefox web browser da sauransu. Ta hanyar amfani da platforms kamar GitHub, suna rubuta code tare, da kuma kara habbaka software da miliyoyin mutane suke amfana dashi. Crowd Sourced Research : Kungiyoyi na fasaha da bincike sunyi koyi da NDC ta hanyar bincike na hadin gwiwa. Platfforms kamar su Zooinverse suna bawa masu aikin sa kai damar yin bincike na fasaha, rarrabe duniyoyi, fassara takardun tarihi da sauransu. Wannan hadin gwiwa daga mutane a fadin duniya yana kara gano abubuwan kimiyya a doron kasa. Remote Creative Teams: A bangare na creative industry, NDC sun hada masu rubuce rubuce, Graphic designers, Mawaka da sauransu don hadin gwiwa wajen yin wani project. Projects din sun hada da rera wata waka wadda za’a yi amfani da ita a wani film, ko yin design na wani website. Wadannan masu hadin gwiwar suna amfani da fasahohi masu karfi sosai domin cima burinsu. A karshe, NDC tana jibantuwa ne ga wani canji a yanayin yadda mukeyin hadin gwiwa wajen yin projects. NDC tana nuna yiwuwar canji na yadda muke tura sakonni, collaborations da sauransu a yanar gizo. Kuma yadda fasaha take kara samun cigaba a kullum, muna sa ran saumun wasu kirkire kirkire masu amfani a nan gaba. @near.brasil.near @near.genadrop.near @cesar667.near @mundoaurora.near @sdq1.near