AI (Artificial Intelligence) kirkirarriyar fasaha ce dake bai wa kwamfuta damar yin tunani, aiki da bada amsar tambayoyi kusan kamar yadda dan Adam zai yi. Ana iya sanya bayanai a cikin kwamfutoci da yawa da kuma horar dasu don gano yadda tsarin abubuwa suke, ta hanyar yin hasashe, da warware matsaloli, har ma su iya nazari daga nasu kura kuran. Fasahar ta dogara ga wasu bayanai da ake kira "Algorithms"- wanda dole ne abi su a yadda aka tsara don a samu kammala aiki. Fasahar itace tushen mataimakan kama-da-wane, misali; Fasahar tana taimakawa Facebook da Twitter wajen bada shawarar abinda kafofin sada zumunta zasu nuna wa masu amfani dasu. Alakar Illia Polosukhin da AI Illia Polosukhin ya kasance daya daga cikin wasu jajirtattun masu bincike a google research su 8, wanda suka rubuta wata takarda mai suna "Attention Is All You Need". Takardar ta kawo wani tsari da ake kira transformer model architecture, Wanda ya kawo canji ga yadda ake yin AI, inda yake bada muhimmanci ga "Attention Mechanism" ma'ana tsarin kirkirar AI daka saka AI ya bada muhimmanci ga bangarorin data masu amfani. Illia ya bude nashi kamfanin wato NEARProtocol bayan yabar google, sannan shine mutum na farko a cikin wadanda suka fita daga google research don fara nasu kamfanin masu aiki akan AI, inda ya nemo kwararru a bangaren distributed systems daga google, Facebook da Microsoft domin tabbatar da cewa NEARProtocol ta kafu. Alakar NEARProtocol da AI ta hadu ne ta hanyoyi masu burgewa, bayan da Illia Polosukhin ya gano cewa Blockchain yana da damar kawo sauyi ga matsalolin data wanda suke kawo cikas ga AI. Hakan yasa NEARProtocol ta kan gaba a kawo wajen zama wa AI ta hanyar Blockchain Operating System wato BOS. Daya daga cikin abubuwan da NEAR take yi yanzu shine kawo hadaka daga web2 zuwa web3. NEARProtocol ta cigaba da shiga gaba wajen kokarin bunkasa karbuwar Fasahar Blockchain da AI a fadin duniya, kasancewar NEAR tanada ecosystem mai karfi da kuma fasaha mai amfani. @nearhausa