Near Digital Collective (NDC) wani project ne da ake kan ginashi akan Near Protocol Blockchain wanda yake yunƙurin tattara masu amfani, masu ruwa da tsaki, mamallakan projects, developers da abokan hada gwiwa na Near Protocol Blockchain wuri daya domin gina tsarin da zai baiwa kowanne daga cikin wadannan mutanen damar bada gudummawa wurin gudanar da tsare-tsaren tafiyar da wannan Blockchain din na Near Protocol. A ƙokarin da ake na gina al'umma mai gaskiya da rikon amana, da kuma tabbatar da cewa NDC ta kunshi masu kaifin tunani don cigaba da tabbatar dashi NDC ta qaddamar da wani tsarin tantancewa mai suna IAM HUMAN VERIFICATION. IAM HUMAN VERIFICATION wani tsari ne da ake amfani dashi don tabbatar da masu amfani da Near da kuma son shiga cikin tsarin NDC lallai mutane ne ba bots ba. Tsarin IAM HUMAN ya bada gudummawa ta yadda za a iya amincewa da mutum don gudanar da aiki wa al'umma ko kuma ya cancanci karɓar kudi don yin wani aiki na inganta community. Tsarin tantancewa na IAH yana da amfani guda biyu:- 1. Yanada amfani ga Near community 2. Yanada amfani ga member na Near community Amfanin IAH verification ga near community shine yana rage rashin amana kuma yana tabbatar da amana a tsakanin kungiyoyin Grassroots wadanda suka hadu suka samar da Near ecosystem. Yana bada tabbacin cewa masu aikin tabbatar da inganci hada - hada (validators) mutane ne ba robots ba. Har ila yau tsarin yana samar da yanayin aiki mai sauki domin tabbatar da aikin DApps da habaka ayyuka akan Blockchain din. Amfanin sa ga mutum ko member na Near protocol kuma shine yana daukar mai shi zuwa matakin amana, yana bada ƴancin yin zaben wanda aka fi so, yana bada damar mallakar Token na Soul Bound (SBT), yana kuma bada damar tsayawa takara a kowanne matsayi da ake so a near Protocol, sannan kuma yana bada dama don gina aiki akan Blockchain na Near Protocol. Al'umma zasu iya bayar da gudummawa wurin tabbatar da NDC ta hanyar yin IAM HUMAN VERIFICATION, zama a fadake ta wajen bibiyar abubuwan da suke faruwa a cikin Near ecosystem, wannan ya hada da Near social, website na near da kuma kafafen sada zumunta na Twitter, telegram da sauran su, bada gudummawa a abubuwan da ake ganin zasu kawo cigaba a Near Protocol. Hakika a koda yaushe gina community yana da matukar amfani, Yanada kyau mu jawo duk wani da muka san Yanada sha'awar abubuwan da suka shafi web3, ko developer ne ko normal user duka su zo ayi wannan tafiyar tare, duba da yanayi mai sauki da alkhairai da Near tazo dasu. @nearhausa