Menene Smart contracts Smart contracts umurni ne da ake ajiye shi a cikin Blockchain, a jikin sa za a rubuta duk dokoki da tsarika da ake so su faru gidan wasu sharuda sun cika. Smart contracts script ne ko wani jerin umurni da ake ba komfuta wanda ake kiransu da code. Misali kamar mutum yace idan followers din sa suka kai guda 1000 zai raba musu 1m ta yadda kowa zai sami 1000. Amma kuma mutumin daya fadi haka taya za a san tabbacin cewa zai bada kudin ba tare da an shigo da shari'a ko doka ba tun da ai babu wanda yasanshi. Toh anan smart contracts zai yi aiki, za a shigar da sharadin da ake buqata ya cika, da number asusun banki na mutanen da za a rabawa kudin, da adadin kudin da za a raba, duk za a saka a cikin smart contracts din. Za a saka umurni ko code wanda da zarar sharadin ya cika za a turawa kowa kudinsa koda kuwa wanda ya sanya sharadin yana nan ko baya nan, koda yardar sa ko babu, kuma bazai iya canzawa ko ya dakatar ba. Toh da zarar wannan sharadin ya cika komfuta zata sani kuma zata turawa kowa kudin sa nan take. Sannan kuma kowa zai iya duba cikin smart contracts din yaga abinda aka saka a ciki. Smart contracts ba kamar contracts din shari'a bane hasali ma anyi shi ne don kar a buƙaci lauya ko alƙali ko hukuma, tun da da zarar an yarda da abinda ke ciki da kansa zai aiwatar da komai. Smart contracts akan Near Protocol NEAR Protocol suna bayar da framework mai karfi inda developers zasu kirkiri decentralized applications dApps masu amfani da smart contracts kuma masu aiki a wajaje da yawa. Misalin manyan abubuwan da smart contracts ke badawa a Near su ne kamar haka.. 1. Scalability: Sharding architecture na NEAR Protocol yana bawa smart contracts damar faruwa a tare, cikin hanzari kuma da tabbatar da cewa mutane da yawa zasu iya yin hada hada da yawa a lokaci a cikin sakan daya. Wannan damar, ta tabbatar da cewa manhajoji a kan NEAR zasu yi amfani komin yawan mutanen da suke kan su. 2. Rashin Tsada: Tsarin tattalin arzikin NEAR yana tabbatar da cewa za’a iya yin duk hada hadar da za’a yi cikin kwanciyar hankali ba tare da ana tunanin tsada ba. Developers zasu iya rubuta smart contracts dinsu sannan suyi amfani da blockchain din ba tare da sunyi tunanin tsadar gas fee ba. Hakan ya kawo sauki gare su da kuma sauran mutane masu amfani da manhajojin. 3. Tsaro: NEAR Protocol sun bada muhimmanci sosai ga tsaro, inda suka tabbatar da wani mechanism mai karfi domin bawa smart contracts tsaro da kuma magance matsalolin da zasu zo a gaba. Ta hanyar verification, auditing da kuma best practices na smart contract development, NEAR suna da niyyar kawo fage mai tsaro domin wallafa manhajoji masu yin aikin da aka kirkire su domin shi. 4. Usability: NEAR suna bada muhimmanci sosai ga jin dadinn developers wajen kirkirar manhajojin su domin ta yin hakan ne zasu samu damar kirkirar manhajojin cikin kwanciyar hankali. Shi yasa suka dage tukuru wajen kawo tools masu yawa, documentation da kuma libraries domin taimakawa wajen kirkirar smart contracts. Haka zalika, kasancewar NEAR sun kawo manya manyan sanannun frameworks da IDE (integrated development enviroment) ya kawo sauki wajen developing manhajojin. 5. Interoperability: NEAR Protocol an yi shi ne da niyyar samar da sauki wajen interoperability, hakan ya bawa smart contracts din da suke kan NEAR damar yin interaction da smart contract din da suke kan sauran blockchain cikin sauki. Amfanin smart contracts akan Near kuma su ne kamar haka - Decentralized Finance (DeFi): Smart contracts, sune kashin bayan da ke tafiyar da harkan decenralized finance kamar su lending and borrowing platforms, decentralized exchanges (DEXs), da sauransu. - Management na Supply Chain: Ta hanyar recording na transactions a ledger domin kasancewa kowa yana iya ganin su, a kan yi amfani da smart contracts wajen tracking na kaya daga inda a ka loda su zuwa inda za’a kai su a duk fadin duniya. Hakan yana rage zambo kuma yana tabbatar da transparency. - Buga wasanni (Gaming): Ana amfani da smart contracts wajen kirkirar decentralized gaming platforms, hakan yana bada dama ga masu buga wadannan wasannin wajen yin cinikayyar in game assets. Misali (NFT’s na Zomland). @nearhausa