Nodes wasu tarin na'urori ne ko kuma ace komfutoci wanda ake linking dinsu da Blockchain don su tabbatar da ingancin ko wani bayani kafin su tabbatar da wanzuwan sa akan Blockchain. Duk wani bayani ko transaction da za a daura shi akan Blockchain ba kai tsaye yake tafiya kan Blockchain ba dole sai wadannan masu running node din sun tantance ingancin sa sun tabbatar da cewa akwai sahihin labari ko sahihin transaction kafin su bari shi wannan bayani ko transaction din ya wanzu akan Blockchain din. Mutane suna running node saboda dalilai kamar haka 1. Domin Karawa Network Tsaro: Wasu suna running node wanda ake kira ‘validator nodes’. Wadannan nodes din suna taimakawa Near wajen tabbatar da tsaro sannan su kuma su sami wani lada na aikin da suke yi. 2. Domin sauri wajen shiga wasu manhajoji: Akwai nodes da ake kira RPC (remote procedure call), wadannan nodes din suna kara sauri da availability na wasu manhajoji na musamman. 3. Domin yin Kirkire-kirkire: Developers zasu iya amfani da abinda ake kira localnet node. Shi wannan localnet node din yana basu damar gwada abubuwan da su ka kirkira a ‘Controlled environment’ kafin a sake su a mainet. 4. Domin yin analysis a kan data: Wasu analysts din su kan yi amfani da Archival node (node din da yake kunshe da duk wani tarihin hada-hadar da aka yi a kan blockchain. Ire-iren nodes guda uku ne kuma NEAR Protocol na amfani da su duka. 1. Validator Node: Wadannan sune manya manyan masu kula da harkokin NEAR, su suke da alhakin yanke muhimman shawarwari da kuma kirkiro sabbin blocks. 2. RPC Nodes: Wadannan nodes din suna bawa developers hanyar samun damar amfani da wasu bangarori na NEAR Protocol. 3. Archival Node: Wannan node din shi ne yake da alhakin ajiye gaba daya tarihin hada hadar da aka taba yi a kan blockchain, wanda yake taimakawa wajen yin analysis din abun da ya faru a baya, da abunda ya ke faruwa a yanzu. Near Protocol suna da network kala-kala wanda suka hada da 1. Mainet: Wannan shine asalin network din inda ni da ku muke yin transactions a yau da kullun. 2. Testnet: Network din da developers su ke amfani dashi waje gwada abubuwan da suka kirkira kafin su sake su ga jama’a. 3. Betanet: Wannan yana yanayi da testnet saidai shi wannan anyi shi ne don gwajin sabbin tsaruka da akan kara a manhajoji kafin a sake su ga jama’a. 4. Localnet: Wannan network ne da developers su ke amfani dashi wajen gwada abubuwan da suka kirkira a boye, ba tare da sun bayyana shi don amfanin jama’a ba. @nearhausa