@Nearhausa.near NEAR PROTOCOL!!! Near Protocol wani blockchain ne mai zaman kanshi wanda yake da saukin amfani, environment friendly (baya bukatar na’urori masu karfi wajen aiki) wanda aka gina shi tun asali da sauri, tsaro, da kuma daukar nauyi mai yawa kuma anyi shi ne a kan tsari sabo mai ma'ana, NEAR, layer one blockchain ne wanda yake kan tsarin proof of stake kamar Ethereum, kuma yana amfani da wata sabuwar fasaha wai ita sharding wajen kammala transactions dinsa sannan kuma developers dinshi sun bada muhimmanci a wajen saukin yin amfani ga masu amfani dashi gaba daya. Yana da kyau mutum ya sani Near account na amfani ne da account abstraction, ya sauwaka wa user yanda sauran blockchains suke amfani dashi kamar 0x9A466804Fd8A2d811cFE9866a3AD62a9740dD804, inda suke amfani da named account kamar shsfsks.near wanda yafi saukin ganewa da kuma saurin haddacewa, wato hakan yana nufin ana gane account da suna ne bada numeric ko numbers ko alphanumeric ba kamar sauran Blockchain, Bude account a NEAR bashi da wahala sam inda kai zaka iya bude shi kai tsaye zuwa wallets site nasu kamar Meteor, Here sender ko Hot (tg) da sauransu, sannan kuma yana da saurin wajen kammala transactions (kusan sakan ,1.3) sannan bashi da tsada wajen transactions (kasa da cent 1). Near nada juriya saboda acikin shekara hudu da kirkirar NEAR, ya shiga cikin jerin blockchain wanda basu taba samun downtime ba, wato babu wata rana da NEAR protocol suka taba samun tangardar transactions, kuma daga wannan lokacin zuwa yanzu, NEAR sunyi kammala transaction sama da miliyan 800 wanda da yawa daga cikin wadanda suka yi wadannan transactions din basu san ma sun yi ba. A shekarar 2023 akwai lokacin da sai da aka samu transactions guda miliyan 13 a rana daya. A watan mayun shekarar 2024 kuwa, NEAR sun dora manyan dApps guda uku kamar Kai-ching, Sweat da kuma Hot Wallet. Shiyasa na zabi near protocol's akan sauran Blockchain.