@nearhausa chain Abstraction Chain Abstraction shine abinda zai karya barrier wanda yake hana mutane shiga web3 sosai. Ya kara da cewa rabe-raben blockchains shine yake kara tokare sabbin shiga wajen amsar wannan fasahar ta web3. Idan a ka saukaka wa mutane hanyar shiga da kuma bawa developers saukin kirkire-kirkiren su a industry din gaba daya, toh karbuwar web3 zai karu sosai. Kuma hakan zai yiwu ne ta hanyar Chain Abstraction (Chris Donovan). Tun shekarar 2018, developers din NEAR protocol sun Ƙirƙire shi ne da niyyar tabbatar da chain abstraction a gaba, tare da bawa daɗin amfani muhimmanci wajen kirkirar dApps, samar da account daya mai amfani a chains da yawa, da kuma blockchain wanda zai iya kammala hada hadar mutane da yawa a lokaci daya. A halin yanzu, an kara Near, da hadin gwiwar Frontier Research da kuma Agoric, sun kadddamar da ranar chain abstraction a taron ETHDenver da akayi a wata March. Inda aka samu mutane 1200 wadanda suka halarci wannan taron. Wannan taron ya kawo manyan mutane a duniyar blockchain da developers da kuma sauran jama’a wanda suka hada da Sreeram Kannan daga EigenLayer da kuma Adrian Brink daga Anoma. Anyi hirarraki da hadin gwiwa masu amfani inda a ka tattauna ci gaban web3 da kuma yadda za ta kasance a nan gaba. Ba’a tsaya haka nan ba, mun sami ganin nunin yadda ake yin trasnaction a kan BNB blockchain da $SWEAT cikin sauki ba tare da matsalolin signing trasnactions ko biyan gas fee ko kuma canji daga NEAR chain zuwa BNB chain ba. Wannan shine abinda hada hadar mu ta blockchain zata zama nan gaba. Daya daga cikin manyan abubuwan da suka faru shine bayyana tsarin cake da aka yi (ba cake din ci ba tallman). Wannan tsari ya kara fadada fahimtar chain abstraction da kuma yadda za’a ci gaba da habbaka shi. Bayanan da aka yi sun hada da bayani a kan threshold signatures, multi-chain settlements da kuma abstracted security. Sannan a kaddamar da cake working group wato wasu mutane wanda aikin su shine tabbatar da ci gaban chain Abstraction. A taron BUIDL Asia A birnin Seoul na Kasar Korea, Co-founder na NEAR Foundation kuma CEO Illia Polosukhin ya bayyana wani sabon tsari wanda zai taimaka wajen tabbatar da chain abstraction wato chain signatures. Wannan tsari abu ne mai ban sha’awa saboda yana bawa NEAR accounts, da smart contract damar yin transactions a kan ko wane irin blockchain. Wannan yana faruwa ne da taimakon wani network wai shi MPC wato ‘Multi Party Computation’. Hakan yana nufin NEAR accounts zasu iya yin transactions a kan wasu blockchains din kamar Bitcoin da Ethereum. A taron BUIDL Asia A birnin Seoul na Kasar Korea, Co-founder na NEAR Foundation kuma CEO Illia Polosukhin ya bayyana wani sabon tsari wanda zai taimaka wajen tabbatar da chain abstraction wato chain signatures. Wannan tsari abu ne mai ban sha’awa saboda yana bawa NEAR accounts, da smart contract damar yin transactions a kan ko wane irin blockchain. Wannan yana faruwa ne da taimakon wani network wai shi MPC wato ‘Multi Party Computation’. Hakan yana nufin NEAR accounts zasu iya yin transactions a kan wasu blockchains din kamar Bitcoin da Ethereum. Tare da Chain Signatures, akwai kuma abinda ake kira Multichain Gas Relayer. Wannan yana cire bukatar tokens su rinka biyan gas fee a kan chains kala kala. A saukake zaka iya biyan gas fee da NEAR a ko wane blockchain. Projects din da suke amfani da chain signatures sun hada da Sweat Economy, East Blue, Linear, Mintbase dama wasu projects. Chain Signature ba karamin taimakawa web3 zai yi ba wajen maida amfani da manhajojin web3 cikin sauki. Wannan ci gaban ya shafi masu amfani da manhajoji (users) da kuma masu kirkirar wadannan manhajojin (developers) inda hakan zai bude sabuwar hanyar amfani, yin transactions da kuma kirkire-kirkire a kan open web.