@NearHausa ARTIFICIAL INTELLIGENCE Fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta Artificial Intelligence (AI) tana habaka cikin sauri, kuma tana canza yadda ake gudanar da abubuwa da dama na rayuwar zamani. AI yana bai wa kwamfuta damar yin tunani, aiki, da ba da amsar tambayoyi kusan kamar yadda Dan Adam zai yi. Ana iya sanya bayanai a cikin kwamfutoci da yawa da kuma horar da su don gano yadda tsarin abubuwa su ke, ta hanyar yin hasashe, da warware matsaloli, har ma su iya nazari daga nasu kura-kuran. Fasahar ta dogara ga wasu bayanai da ake kira, algorithms - wadanda wasu jerin dokoki ne da dole ne a bi su a daidai yadda aka tsara don a sami kammala aiki. Fasahar ita ce tushen mataimakan kama-da-wane masu sarrafa murya kamar su Siri da Alexa. A watan december na shekarar 2017, wasu jajirtattun masu bincike su takwas a google research, sun rubuta wata muhimmiyar takarda mai suna “Attention is All You need”. Wannan takardar ta kawo wani tsari ne wanda ake kira transformer model architecture. Wannan tsari ya kawo canji ga yadda ake yin AI (Artificial Intelligence) inda yake bada mahimmanci ga: Tsarin kirkirar AI inda ake saka AI ya bada muhimmanci ga bangarorin data masu amfani. Transformers sun taka muhimmiyar rawa a bangaren AI musamman wajen ‘Machine translation’ domin fassara yare kala kala (misali google translate), text summarization da kuma question answering wato robot mai bada amsoshi. Abun lura a nan shine wanna Transformers din su ne suka taimaka wajen kawo mana AI kamar ChatGPT, Bard da saurans Illia Polosuhkin, wanda ya kasance daya daga cikin wadannan masu binciken, shi ne na farko a cikin wadanda suka fita daga google research domn fara nasu kamfanonin masu aiki a kan AI. Bayan Illia ya bar google, yaje ya bude nashi kamfanin wato NEARProtocol inda ya nemo kwararru a bangaren distributed systems daga google, Facebook da microsoft domin tabbatar da cewa NEARProtocol ta kafu. Near, ta samu goyon baya daga manyan Venture Capitalist kuma ta nuna kanta a matsayin mai taka muhimmiyar rawa a duniyar blockchain inda a yanzu ita ce blockchain ta 38 a duniya da market cap na biliyan $1.4. Labarin NearProtocol ya hadu ne da AI ta hanyoyi masu ban sha’awa: Illia Polosukhin ya gano cewa blockchain yana da damar kawo sauyi ga matsalolin data wanda suke kawo cikas ga AI. Hakan ya sanya Near Protocol ta zamo ta kan gaba a kawo gadon zama ga AI ta hanyar blockchain operating system wato BOS. Daya daga cikin abubuwan da NEAR take yi a yanzu shne kawo hadaka daga web2 zuwa web3. Musammamn ta wajen kirkirar dApps masu kama da manhajojin da muke amfani da su a web2 kamar twitter a matsayin Near Social. Co founder na Near wato Alex skidanov shima ba’a barshi a baya ba inda ya shiga bincike tukuri domin kawo wata sabuwar AI mai suna Jasnah, inda yake bada muhimmanci wajen kirkirar manyan language models. Decentralized approach na jasnah, tare da amfani da community mai karfi na NEAR, ba karamin kaimi zasu kara wa blockchain da kuma AI ba. Near protocol ta ci gaba da shiga gaba wajen kokarin bunkasa karbuwar fasahar Blockchain da AI a fadin duniya. Kasancewar NEAR tana da ecosystem mai karfi da kuma fasaha mai amfani, Masu hasashe sun ce Near zata zama blockchain ta kan gaba wajen bunkasa fasahar blockchainn gaba daya.