Gamemmen Guziri dan Sanin Near Protocol. A kwana a tashi mutane na qara fahimta da sake kutsawa cikin ayyukan #BlockChain da #AI dan ganin anfaninsu da yadda mutane ke samun sauqi wajen al-amaransu dama 'yanci dogaro da kai a fannin tattalin arziki, ba a nan kadaiba, hada da samar da tsaftaceccen matsuguni daga annobar dumaman yanayi da makamantansu. Wannan yabawa Maqeran Manhajar Near zuwa da vangarori da dama da magance matsalolin mutane na yau da kullum wadanda wasu Blockchain da AI ecosystems suke da rauni wajen yin hakan. A takaiceccen takaitawa, kubiyomu @nearhausa.near dan samun fayyaceccen bayanai akan haka. Kafin nan, adan lashe wannan dan samun abun guziri. Near Protocol Near Protocol wani blockchain ne mai zaman kanshi wanda yake da saukin amfani, environment friendly (baya bukatar na’urori masu karfi wajen aiki) wanda aka gina shi tun asali da sauri, tsaro, da kuma daukar nauyi mai yawa. NEAR, layer one blockchain ne wanda yake kan tsarin proof of stake kamar Ethereum, kuma yana amfani da wata sabuwar fasaha wai ita sharding wajen kammala transactions dinsa sannan kuma developers dinshi sun bada muhimmanci a wajen saukin yin amfani ga masu amfani dashi gaba daya. Ya kasance za6inka saboda NEAR anyi shine a kan tsari sabo wanda an gwada shi kuma an ga zai iya. Anyi shi a kan tsari mai ma’ana inda aka yi mai fasali da abubuwa kamar named account da account abstraction. Haka zalika ba’a bar dvelopers a baya ba domin NEAR ya basu infrastructure mai karfi domin kirkirar manhajojin su cikin sauki, daga smart contracts, zuwa indexers tare da tabbatar da compatibility tsakanin shi da sauran blockchains. Ba iya nan kadaiba, wannan Manhaja nada Sauqin Anfani, Juriya, Qarancin Cutarwa ga Muhalli, Tsaro da bada dama ga Maqera na musamman dan qereqerensu.