Daga bakin masu shi! Masu abuand da abunsu!! Bayani Gamsasshe daga masu shi!!! A taron BUILD Asia A birnin Seoul na Kasar Korea, Co-founder na NEAR Foundation kuma CEO Illia Polosukhin ya bayyana wani sabon tsari wanda zai taimaka wajen tabbatar da chain abstraction wato chain signatures. Wannan tsari abu ne mai ban sha’awa saboda yana bawa NEAR accounts, da smart contract damar yin transactions a kan ko wane irin blockchain. Wannan yana faruwa ne da taimakon wani network wai shi MPC wato ‘Multi Party Computation’. Hakan yana nufin NEAR accounts zasu iya yin transactions a kan wasu blockchains din kamar Bitcoin da Ethereum. Yadda Wannan Fasaha Ke Aiki NEAR account, wanda zai iya zama smart contract zai nemi izini a wajen validators ko MPC nodes domin yin transactions a kan wasu blockchains din. Hakan yana yiwuwa ne ba tare da mutum ya sauka zuwa wancan blockchain din ba, kuma ba sai yana da account a wancan blockchain din ba. Da account daya, mutum zai yi hulda da blockchain kala kala. Wannan yana da bambanci da sauran MPC networks saboda anyi shi ne saboda accouns, ba deposit, ko bridges ba. Wannan ba karamin abu bane a duniyar Decentralized Finance (DeFi) saboda yana kawo sauki wajen amfani da wasu assets da suke kan wasu blockchains din. Misali, zaka iya amfani da XRP (ripple) domin aron USDC ko kayi trading Doge domin a baka Solana. Da dai makamancin hakan. Wannan MPC network din da yake taimakawa domin tabbatar da Chain Signatures ya samu ikon faruwa ta dalilin hadin gwiwar da aka samu tsakanin NEAR da Eigenlayer, Kuma stakers na Eigenlayer da NEAR su suke basu tsaro, kuma a nan gaba, za’a sashi ya zama a bude domin amfanin sauran jama’a Tare da Chain Signatures, akwai kuma abinda ake kira Multichain Gas Relayer. Wannan yana cire bukatar tokens su rinka biyan gas fee a kan chains kala kala. A saukake zaka iya biyan gas fee da NEAR a ko wane blockchain. Wannan ba karamar dama ya kawo wa developers ba saboda hakan yana nufin zasu iya kirkirar manhajoji da suke aiki a kan ko wane irin blockchain ab tare da sun bukaci bridges ba. Sauran mutane kuwa (ni da ku kenan tallman) zasu iya manajin gaba daya cryptocurrency dinsu ko NFT na ko wane chain a account daya ba tare da rarrabe-rarraben account ba. Wasu daga Projects din da suke amfani da chain signatures sun hada da: - SWEAT East - East Blue - LiNEAR - Mintbase Chain Signature ba karamin taimakawa web3 zai yi ba wajen maida amfani da manhajojin web3 cikin sauki. Wannan ci gaban ya shafi masu amfani da manhajoji (users) da kuma masu kirkirar wadannan manhajojin (developers) inda hakan zai bude sabuwar hanyar amfani, yin transactions da kuma kirkire-kirkire a kan open web. Agarzayo @nearhausa.near dan Jin cikakkakun bayanai akan wannan fasahar.