Alaqar Artificial Intelligence (AI) da NearProtocol Artificial intelligence da akafi sani da AI, yakasance wani qerarran fasaha ne dayake aiki gwargwadon yadda 'dan Adam keyi wajen Ansa tambaya, aiwatar da aiyuka bisa umarni da sauqaqa aiyuka akan kwanfutoci da makamantansu. Ilimin AI yasamu karfafuwa ne da samun sauyin tsari bayan samuwar littafin ATTENTION IS ALL YOU NEED, wanda hamshaqan masu bincike guda takwas a Babban Manhajar Bincike ta Goggle suka wallafa a shekarar 2017, wanda Illia Polosukhin yakasance daya daga acikin wadannan mutane. Illia Polosukhin yazamo na daya da yabar Goggle saboda kyakkyawar fahimtar da yayiwa Attention is all You Need, kasancewarsa littafin dayakawo tsarin Transformer Model Architecture (tsarin da yakawo sauyi wajen qirqirar AI) wanda yabada muhimmanci kan tsarin Attention MECHANISM. Hakan yasa Illia Polosukhin da abokinsa Alex Skidanov fara kirkirar manhajarsu ta NearAI, daga bisani ta koma Near Protocol. Cikin bincikensa, Mr Polosukhin ya gano cewa AI na fama da cikas wajen kawo sauyi a bayanai (wato Data), sa6anin Blockchain inda yakeda damar yin hakan. Hakan yasa shi hade fasahohin biyu akan manhajarsu ta Near Protocol dayasa tazamo daga gaba gaba wajen tabbatuwan AI akan Blockchain Operating System (wato BOS). Saboda samun cikakkakun bayanai, kubiyomu kafafenmu nasada Zumunta ta @NearHausaa dan ganawa dakuma ji daga kwararraru.